chat An ba da rahoton Shema ya kai kansa EFCC


​Rahotanni daga Nigeria sun ce da safiyar yau tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema, ya kai kansa ofishin hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati.

Wadansu majiyoyi a hukumar ta EFCC sun tabbatar wa BBC cewa yanzu haka tsohon gwamnan yana ofishin, inda yake rubuta jawabi ana kuma yi masa tambayoyi.

A jiya ne dai tsohon gwamnan ya musanta sanarwar da EFCC ta fitar ranar Laraba cewa ba ta san inda yake ba, don haka tana neman shi ruwa-a-jallo.

Hukumar dai na neman Shema ne game da zargin yin sama da fadi da wasu makudan kudin Jihar ta Katsina.

*bbc

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s