Yadda Zaven Burin Zuciya Na Qasa Ya Kafa Tarihi

img-20161107-wa0012.jpg

Majalisar Burin Zuciya ta Qasa ta gudanar da zaven Shugabanta na Qasa a karo na farko tun bayan kafuwar Majalisar yau kimanin shekaru takwas kenan da suka gabata, zaven wanda shi ne irinsa na farko da wata Qungiya mai zaman kanta ta tava gudanarwa a tarihin Qasar nan, musamman idan akayi la’akari da yadda tun farko aka shirya gudanar da zaven dai-dai da yadda kundin tsarin mulkin Qasar nan ya tanadar.

Zaven Shugaban Majalisar ya gudana ne a ranar Asabar 5/11/2016, wanda aka gudanar a duk faxin Qasar nan mai jihohi 36 da Abuja, sannan zaven ya gudana a Qasar Nijar. Sannan an shirya duk wasu kayan zave dai-dai da zamani, domin hatta su kansu jami’an zaven qarqashin jagorancin Shugaban Kwamitin Zaven na Qasa, Kwamared Auwal Kontagora, tun ranar juma’a, suka iso Garin Kaduna xauke da takaddun zave, amma saboda tsatssauran matakan tsaro, babu wanda zai iya shaida maka cewa, ga takamammen otel xin da suka sauka, duk wannan an shirya shi ne domin gudun samun maguxi.

A Jihar Kaduna, an gudanar da zaven a ofishin Majalisar Burin Zuciya dake kan titin Katuru dake Badarawa tsakiyar Garin Kaduna. Kuma ya sami halartar ximbin mambobin Majalisar, duk da kasancewar an tsaurara matakan tsaro, domin babu abin da idonka ke hangoma illa jami’an ‘yan sanda dauke da bindigogi, domin shirin ko ta kwana, amma cikin ikon Allah an gudanar da zaven cikin kwanciyar hankali da lumana.

Ranar lahadi 6/11/2016, rana ce ta musamman wanda aka ware domin sanar da sakamakon zave, wanda tun da farko an shirya za’a gudanar da sanarwar sakamakon zaven a ofishin Majalisar dake titin Katuru Badarawa cikin Garin Kaduna, amma saboda wasu dalilali irin na matakan tsaro na sirri, ya sanya aka sauya wajen sanar da sakamakon zaven zuwa Sakatariyar Qungiyar ‘Yan Jaridu na Qasa reshen Jihar Kaduna, wanda a can ma an tsananta matakan tsaro sosai, domin babu wanda aka baiwa izinin shiga wajen, sai jami’an zaven, wakilan ‘yan takara, da kuma ‘yan jaridu.

Tun da farko da yake gabatar da yadda zavukan suka gudana, Shugaban hukumar zaven ta Qasa, Kwamared Auwal Muhammad Kontagora, ya bayyana cewa, kusan kimanin watanni huxu suka kwashe suna bitar yadda zavukan zasu gudana.

Kwamared Kontagora ya ce, “Mun xauki kimanin watannin huxu muna bitar yadda wannan zave zai gudana, kuma Alhamdulillah, munyi iya bakin qoqarinmu sauran kuma mun barma Allah. Inaso na tabbatar maku da cewa jiya Asabar 5/11/2016, muka gudanar da zavukan Shugaban Majalisar Burin Zuciya na Qasa, wanda ya gudana a faxin Jihohin 36 da kuma Abuja, sannan zaven ya gudana a Qasar Nijar.”

“Sannan mun wakilta wakilan ‘yan takara har mutune biyu a duk jihohin da aka gudanar da zavuka, domin su kasance wakilai ga ‘yan takaransu. ‘Yan takarar dai sune, Alhaji Habeeb Nalele daga Jihar Filato, da kuma, Malam Ibrahim Indabo daga Jihar Kano, wanda dukkaninsu sai da muka tantance su, sannan suka sami damar tsayawa wannan takara.

Alhaji Habeeb Nalele ya sami quri’u 1,111.

Malam Ibrahim Indabo ya sami quri’u 330.

Saboda haka, ni Kwamared Auwal Muhammad Kontagora, zan yi amfani da wannan dama da doka ya bani na sanar da cewa, Alhaji Habeeb Nalele daga Jihar Filato, shi ne wanda ya lashe zaven Shugaban Majalisar Burin Zuciya na Qasa, da Quri’u 1,111. A yayin da ya kayar da abokin takararsa, Malam Ibrahim Indabo daga Jihar Kano, wanda ya sami quri’u 330.

A yayin da yake sanya albarkacin bakinsa jim kaxan bayan an sanar da sakamakon zaven, Editan Jaridar LEADERSHIP Hausa, Malam Musa Muhammad, ya bayyana matuqar farin cikinsa a fili, bisa yadda aka gudanar da zaven cikin kwanciyar hankali, sannan ya miqa fatan alherinsa ga dukkan mambobin majalisar Burin zuciya dake faxin Nijeriya da kuma Qasashe waje, sannan ya bayyana cewa, Insha Allah yana tare dasu xari bisa xari.

Shima a nasa tsokacin, Shugaban kwamitin Amintattu na Majalisar, Alhaji Mahmud Indabawa(Dattijon Burin Zuciya), ya miqa godiyarsa na musamman ga Shuganan Rukunonin Kamfanin Jaridar Leadership, Mista Sam Inda Issiah, a bisa yadda ya basu dama suke gudanar da harkokinsu a wannan jarida ba tare da suna biyan ko sisi ba, a cewarsa, wannan ba qaramin abin alfahari ba ne. Sannan ya miqa godiyarsa da fatan alheri, ga madugu uban tafiya, Alhaji Al-amin Ciroma, wanda a cewarsa, shine silar duk wani quluwar zumunci dake gudana a wannan Majalisa.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s