Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Haramta Duk Wani Nau’i Na Taro Da Zagaye Kan Titi Ba Tare Da Izini Ba

elrufai-office

 

Gwamnatin Jihar Kaduna ta haramta duk wani nau’i na tattaki ko wani nau’i na taro ba tare da izini ba. Wannan sanarwar ta dokar ta fito ne jiya a wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar. Don haka ake bukatar jama’a su yi biyayya ga dokar har zuwa lokacin da za a dage wannan dokar.
Wannan dokar ta biyo bayan taron da masu ruwa da tsaki a kan tsaro a Jihar Kaduna suka yi jiya. A nan ne aka shawarce Gwamnatin Jihar Kaduna da daukan wannan mataki na hana duk wani taro ba tare da izini ba na wani dan lokaci saboda tsaro.


Bisa wannan dalilin ne gwamnatin ta karbi wannan shawara kuma ta fitar da wannan sanarwar ta hannun mai magana da yawun gwamnan, Samuel Aruwan.


“An dauki wannan matakin ne don kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kaduna baki daya”.
“Sannan kuma jami’an tsaro an ba su ragamar tabbatar da an bi wannan dokar. Kuma an shawarce kowa ya ci gaba da hidimarsa ta yau da kullum tare da zama lafiya da juna”.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s