Yan’uwan ta Buhari 50,000 yi masa addu’a ya waraka

buhari-daura-prayers-2

A ci gaba da nuna goyon baya wajen yima Shugaban Kasa Muhammadu Buhari addu’oin samun sauki da kuma fatan alheri, a qalla sama da mutanen dubu 50,000, Maza da Mata har da tsofaffi  a qarqashin jagotancin Qungiyar Matasa masu kare manufofin ci gaban ayyukan alheri na  Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda a turance ake kira da Buhari Youth Congress for Change (BYCC), na kasa reshen Garin Daura dake Jihar Katsina, suka gudanar da addu’oi na musamman domin samun lafiyar Shugaban Kasa Buhari.

A yayin da yake jawabi a wajen gangamin, Shugaban Qungiyar BYCC da kuma Daura social media forum, reshen Daura, Malam Musa Badamasi Daura, ya bayyana cewa, sun gabatar da wannan addu’oi ne na musamman domin nuna cikakken goyon bayansu ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a bisa irin qudurorinsa na alheri ga ‘yan Nijeriya, wanda suke roqon Allah da ya ci gaba da yi masa jagora domin ya qarasa irin ayyukan alheri da ya dauko yima ‘yan Nijeriya.

Sannan ya bayyana goyon bayansa a bisa yadda shugaban kasa Buhari ke ci gaba da yin yaki da masu satar dukiyar kasar nan, a dalilin su na  cin hanci da rashawa, a cewar sa, yin hakan ba karamin nasara ba ne, musamman idan akayi la’akari da yadda wasu azzalumai masara imani suka dade suna wawure lalitar ajihun kasar nan, ba tare da tunanin hakan da su kayi na iya sanya kasar nan cikin wani mawuyacin hali ba.

Malam Musa Daura, ya kuma roqi ‘yan Nijeriya da cewa su ci gaba da marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya domin ganin ya kai Al’ummar kasar nan zuwa ga gaci.

Shima a nasa jawabin, Sakataren Kungiyar BYCC reshen Daura, Kwamared Rabiu S. Fada Daura, ya bayyana irin kyawawan manufofin da Shugaban Kasa Buhari ke da su ga Al’ummar kasar nan, a inda ya bayyana cewa “Tabbas ya zama wajibi mu fito domin nuna goyon bayanmu da kuma yin addu’oi ga Shugaban kasa Buhari, saboda irin kyawawan ayyukan da yayi  ma ‘yan Nijeriya a cikin shekaru daya da rabi, wanda kuma muke da yakinin cewa, Insha Allahu kamin wani lokaci zai kammala duk ayyukan alherin da gwamnatinsa ta qudiri aniyar kammala su.”

Kwamared Fada Daura, ya kuma janyo hankalin ‘yan Nijeriya musamman masu yima Shugaban Kasa Buhari fatan mutuwa, da cewa duk wani Dan kasa na gari, bai ma shugaban shi mummunar fata, sannan sun manta cewa, mutuwa da rashin lafiya duk suna hannun Allah, sannan ai  murnar mutuwa ai murnar banza ce,  domin babu wani wanda zai kasance a wannan duniya ba  tare da mutuwa ta daukeshi ba.

Daga karshe ya mika godiyarsa ga Masarautar Daura a qarqashin jagorancin Mai martaba Sarkin Daura, bisa irin goyon bayan da suka  bayar wajen yima Shugaban kasa Buhari addu’oin fatan alheri, sannan ya kuma gode ma daukacin ‘yan Nijeriya a bisa irin jajircewarsu babu dare babu rana akan shugaban kasa Buhari.

An dai gudanar da addu’oin ne a filin sallar idi dake Garin Daura, sannan akayi zagayen gari,  daga bisa aka wuce zuwa fadar Mai martaba Sarkin Daura.

 

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s