Kamfanin Bizi Mobile Banking Agency Zai Kaddamar Da Sabuwar Fasahar M Cash A Kasuwar Duniya Ta Kaduna

kaduna-trade-fair

Daga Ibrahim Muhammad, Kaduna

Kamfanin Bizi Mobile banking Agency za ta kaddamar da sabuwar fasahar zamani mai suna M Cash, wanda shi ne irinsa na farko a Nijeriya, wanda kamfanin Bizi mobile zai kaddamar a dandalin kasuwar duniya karo na 38th, wato Kaduna International Trade Fair, dake ci a kaduna.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban rikunonin kamfanin Bizi mobile Banking Agency, Alhaji Aminu Aminu Bizi, a yayin da yake zantawa da manema labarai a kasuwar duniya karo na 38th dake ci a kaduna, wanda Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna Architect Barnabas Bala Bantex ya bude bikin kasuwar.

Ya kara da cewa, kaddamar da sabuwar m cash mobile zai kawo saukin rage wahalhalun da ‘yan uwanmu mutanen karkara ke fuskanta a daukacin yankunan da babu bankuna a wajen, saboda samar  masu da saukin rayuwa wajen yin mu’amular kasuwanci irin na zamani.

“Wannan sabuwar fasahar wanda ake kira a turance M Cash, wani hadin gwiwa ne dake tsakanin bankin unity da kuma kamfanin Bizi mobile, wanda suka yi tunanin samarwa ga Al’ummar da basu da lambar ajiya ta banki, kuma zasu iya cire kudaden da aka turo masu daga kasashen wajen ta hanyar yin amfani da shaidar lambar katin sakon da aka turo masu da kudin.”

Ya ci gaba da bayyana cewa, babban dalilinmu na zuwa kasuwar duniya ta kaduna, shi ne domin mu wayarwa mutanen da zasu halarci wannan kasuwa daga ko ina dake fadin duniya, irin ci gaban fasahar zamani da aka samu ta hanyar yin amfani da biyan kudi da kuma cirewa batare da mutum yaje banki.

“Insha Allahu da izinin Allah,  ranar 1 /4/2017, zamu kaddamar da sabuwar cashless policy, wanda zamu wayar ma Al’umma kai da cewa zasu iya cire kudadensu ko tura kudi  ta hanyar yin amfani da layin lambar wayarsu suna kwance a gidajensu  ba tare da sun je banki ba.”

Alhaji Aminu Bizi, ya kuma kara da bayyana cewa, yanzu haka sun kulla yarjejeniya yin aiki kafada da kafada da bankuna 8 dake fadin kasar nan, wanda zasu kasance wakilansu ta hanyar fadakar da jama’a da kuma wayar masu da kai akan abin da ya shafi harkar banking policy.

Shugaban na kamfanin Bizi mobile ya kuma kara da bayyana cewa, kamfanin sa ya kasance wata hanya ta samarwa da matasa ayyukan yi, saboda a cewar sa, kamfanin ya samarwa matasa sama da dubu 100 ayyukan yi dake fadin kasar nan da kuma wasu ‘yan Nijeriya dake zaune a kasashen waje.

Wasu daga cikin manyan bakin da suka sami halartar bikin bude kasuwar duniyar karo na 38th sun hada da, Ministan harkokin kasuwanci da zuba jari na kasa, Mista Okechukwu Enelamah, da kuma wakilan MD NEPC, Mista Segun Arowolo, da kuma Shugaban Nigeria Chamber of Commerce, Industry, Mines and Agriculture, NACCIMA, Cif  BASSEY E.O. Edem, sauran sun hada da Shugaban Kaduna Chamber of Commerce, Industry, Mines and Agriculture (KADCCIMA), Dakta  Muheeba F. Dankaka, da wakilin mai martaba Sarkin  Zazzau, Alhaji Shehu Idris, wanda  Galadiman Zazzau, Alhaji Nuhu Aliyu ya wakilce shi, da dai sauran manyan baki da dama.Kamfanin Bizi Mobile Banking Agency Zai Kaddamar Da Sabuwar Fasahar M Cash A Kasuwar Duniya Ta Kaduna

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s