Ba masarautar kaura ta bani sarautar dan masani ba – Sahabi Liman

 

Daga Shuaibu Ibrahim Gusau

Ganin yadda kura ta turnuke tsakanin masarautar Kauran Namoda da Hamshakin attajirin nan na Kauran Namoda mai suna Sahabi Liman dan Limamin Kaura, wanda har ya jawo masarauta ta bada sanarwan ta tube attajirin dAga sarautar da yake da ita na Danmasanin Kauran Namoda.

Hakan ya sanya wakilinmu jin ta bakin Dan masanin don jin abin da ya jawo tada wannan kura, da yake amsa tambayar wakilinmu Dan masanin na kaura ya bayyana cewa yana so masarautar kaura ta sani cewa ba masarautar kaura ta bashi sarautar Danmasani ba, Fadar mai martaba Marigayi Alh Ado bayaro ya bashi ita a matsayinsa na surukinsa wanda ke auran ,yarsa, ta biyo ta fadar mai marataba Sarkin Musuli.

Dan masani ya kara da cewa wannan sarautar ba sarauta bace wadda ake cire mutun akan ta,don haka masautar kaura bata iya cireshi daga wannan sarautar balle har ace ta sanya wani, kuma yace lokaci ya kure da za,a iya badda wannan suna daga gareshi na Danmasanin kaura.

Dan masanin na kaura ya kara da cewa yana so al,ummar Kauran Namida su sani cewa laifin da yayi har akace an kwace wannan sarauta shine don sarki yace ya cire limami daga limanci shi kuma yace zai gina masa masallaci babba kuma ya bashi limanci, wannan shine kawai laifinsa.

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan matsa Alhji Sani Abubakar Dangawo shine shuban kungiyar kadiriya da tijjajiya ta shu,ara,u bangaren kauran Namoda ya bayyana cewa basu ji dadin abinda masarauta tayi ba domi a cewarsa Dan masani shin Garkuwan shu,ara,u ta kasa wanda shugan kungiyar ta kasa Rabi,u Usman Baba ya bashi don haka su a wajanshu Danmasani yana nan da sarautarsa ta Danmasanin Kauran Namoda kuma suna goyon bayansa Dari bisa Dari.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s