Ban baiwa yansanda kudi don su bugi dan bautar kasa ba – Sahabi Liman

13728928_1172575176117873_868565676544861598_n.jpg

Daga Shuaibu Ibrahim Gusau

Fitatcen Dan kasuwar nan Alhaji Sahabi Danlimamin Kaura ya karyata zargin da ake masa na cewa ya bawa ‘yansanda kudi don su bugi Dan bautar kasa da ya jiwa yarsa rauni saboda tayi laifi a makaranta.

Sahabi liman ya karyata wannan zarginne a lokacin da suke zantawa da wakilinmu a garin Gusau ababban birnin jihar Zamfara.ya kara da cewa yana gida sai yaji yarinya ta dawo tana kuka ya kirata ya tambaye sai ta nuna masa raunin da ta samu saka makon tafiya da guywa da malamin yace tayi a cikin tsakuwa.

Ya kara da cewa ganin irin wannan rauni yasa hankalinsa ya tashi wanda daga bisani sai ya dauketa zuwa Area command,daga nan ne aka bukaci ya kawo kasa yaki zuwa saida yansanda suka sanya hikima irin tasu,tare kuma da gaiyato shugaban makarantar.

Sao wani abon ban mamaki sai ga yan’uwan ‘yan bautar kasa suna zanga zanga wai asakeshi.

Sai dai wani abin bakin ciki shi yadda yan uwansa suka rika aikawa da sako ta social Media ,ma,ana hayar da ake aikawa da sakonni ta zamani suna fadi karya kan abinda basujiba basu ganiba.

Ya kara da cewa har wasu suka rika amfani da Hoton wani mutun a akayowa jinajina da wuka a baya, a legasa, domin harda hotunan motocin legos amma akace wai a garin kaura akayi don kawai a samrda da tashin hankali na kabilanci ko na addini.

Sahabi ya kara da cewa abinda yake fadi shi bai dace ba a makarantu irin na kudi a rika dukan dalibi ko aji masa rauni, domin a cewarsa wannan ba zai sanya yaro ya sami tarbiyan da ake so ya samuba sai dai ya kangare.

Dan haka Dan masanin na kaura Yayi kira da babbqn murya ga wadanda suke da makarantu musamman ma kudi dasu kula da amanar da aka basu kuma kada su bari wadansu da basusan aikiba su zo su bata masu makaranta. Kuma ya nemi hukumomin gwamnati dasu sanya idanu kAn makarantun kudi kada su yarda su barsu kara zube babu doka da Oda.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s