Tsohon Gwamnan jihar Zamfara ya yanke shawaran sauya sheka zuwa APC

apc_logo
Daga Shuaibu Ibrahim Gusau

A karshen wannan makon ne tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Alh Mamuda Aliyu Shinkafi ya bayyana kudurinsa na sauya sheka zuwa jam,iyar APC ga Dubban magoya bayansa a garin Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Tsohon gwamnan ya ce an dade ana. Ta yawo da maganganu ya cewa wai ya sauya sheka,yace abin ba haka yakeba, gaskiyar maganar itace akwai kwamiti wanda ke karkashin Ahmad A.A master da aka tun tubesu su kuma suka zauna don shawara, tare kuma da tuntubar wadanda suka dace don neman shawara.

Cikin dalilan da aka ya bayyana akwai na samarwa al,ummar jihar Zamfara ci gaba da kuma samar da zaman lafiya ga al,ummar jiar ta Zamfara.

Tsohon Gwamnan ya nemi duk magoya bayansa dasu mara masa baya kuma su baiwa gwamnati goyon baya musamman Gwamnatin jihar zamfara.
Shinkafi ya nemi magoya baya bayansa na birne da kauye da cewa da zarar, jam,iyar APC ta shiya to zata sanar don kowanne daga cikinsu ya tafi mazabarsa ya yanki kati.

Tsohon Gwamnnan ya yakoma jam,iyar APC ne tare da duk kan tsofaffin kwamishinoninsa.sai dai ya bayyanawa al,umma cewa basu dawo jam,iyar APC don neman mukami ba sai don ciyar da jihar zamfara gaba da kuma samar da zaman lafiya,kamar yadda aka saba domin a cewarsa jihar zamfara bata saba da rikicin siyasa ba kamar yadda akeyi a wasu gurare,kuma ya kara da cewa a jihar Zamfara ne zaka samu a gida daya zaka samar akwa magoya bayan jam,iyu daban daban kamar yadda abin yake a gidansu.

Shikafi ya bayyana cewa kowa ya sami cewa tun daga kananan hukumomi har zuwa jiha da ma kasa baki daya jam,iyar da suka baro watau PDP tana cikin matsala.
Sai dai Tsohon Gwamnan ya shelanta cewa basu dawo jAm,iyar APC ba wai don neman mukami,ya ce kamar yadda ya fadi a baya sun shigo ne kawai din ciyar da jihar zamfara gaba.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s