Al’ummar Yankin  Kauru Sun Yaba Wa Gwamnan el-Rufai

UBA SANI KAURUA ci gaba da ziyarar gani da ido da Qungiyar Wayar da kan Al’umma akan ayyukan da Gwamnan  Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed el-Rufai, ta keyi, wanda a turance ake kira da Kaduna State Awareness Forum, qarqashin jagorancin  ofishin mai baiwa Gwamna shawara akan harkokin siyasa, Malam Uba Sani, ta ziyarci Qaramar hukumar Kauru dake Jihar Kaduna.

A yayin da yake bayyana maqasudin ziyarar gani da ido na irin ayyukan ci gaba da Gwamnan Jihar Kaduna yake yiwa Al’ummar sa, Shugaban Qungiyar Kwamared Rabiu Xanbaba, ya bayyana cewa, “aikin dake kan wannan Qungiyar shi ne, bin diddigin irin ayyukan da wannan gwamnati keyi, sannan muna ziyarar Al’umma dake zaune a lungu da kewayen wannan jiha, domin jin irin ra’ayoyinsu game da irin ayyuka da kuma qakubalen dake fuskantar wannan gwamnati.”

Kwamared Xanbaba ya ci gaba da bayyana cewa,” haqqinmu ne mu tabbatar da cewa, ko wane xan Jihar Kaduna ya xanxana irin romon ayyukan wannan gwamnati, sannan haqqinmu ne muji irin koken da Al’umma keyi a inda suke ganin ba a yi musu dai dai ba, da kuma inda akayi masu kuma suka nuna jin daxinsu da godiya.”

Suma a nasu jawaban daban daban, Hakimin Kauru, Alhaji Muhammad Yusuf Kauru, da kuma Hakimin Kufana, Mista Sule D. Meteh, sun godewa da irin ziyarar gani da idon da wannan Qungiyar ta kawo masu, sannan sun buqaci gwamnati da ta sanya ido akan ‘yan kwangilar da take baiwa ayyuka, domin wasu ‘yan kwangilar da zarar sun soma aikin sai su watsar. Sannan sun yaba da jin daxinsu a bisa irin ayyukan alheri na ci gaba da gwamnatin Jihar Kaduna ke gudanarwa a ko wane lungu da saqo dake faxin Jihar Kaduna.

Suma a nasu jawaban, Kansilar gundumar Kauru, Honarabul Sulaiman Tanko Gishi, da kuma Shugaban Matasan yankin Kumana, Mista Manasi Baqo, sun miqa godiyarsu ne ga Gwamnan Jihar Kaduna, a bisa ci gaban ayyukan raya karkara da ya kawo masu, irin  ayyukan da suka haxa da; gina masu titi mai tsawon kilomita 45, a yankin Kumana, da kuma samar masu da gada wanda zasu sami damar fitar da kayayyakin abincin da suka noma, sannan an gina masu bohol 23 a yankin kusau, chawai, kauri.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s