Kamfanin Bizi Mobile Ya Samarwa Mata Marayu 1500 Akin yi  A Jihar Kano

bizi mobile kano (2)

A ci gaba da gudanar da ayyukan alherin na taimakon al”umma da ya saba yi a ko da yaushe, kamfanin bizi mobile cashless consultant limited, ya qaddamar da gidauniyar tallafa wa mata  marayu 1500 akan aikin banking agency a jihar kano.

Da yake jawabi a yayin kaddamarwar, Shugaban kamfanin bizi mobile cashless consultant limited, Alhaji Aminu Aminu bizi, ya bayyana cewa, ” maqasudin da yasa nayi tunanin samarwa marayu ayyukan yi, ba komai bane illa yadda na tashi a maraya babu uwa babu uba, kuma yanzu haka akwai marayu dake rayuwa suke ci a karkarshina, wannan dalili ne ya sanya nayi tunanin ganin mun samarwa mata marayu daga shekara 18 zuwa 30 ayyukan yi wanda zasu dogara da shi, wanda tuni mun qaddamar da irin wannan shiri a jihar kaduna.”

Ya qara da bayyana cewa, “Idan kayi la’akari za ka gane cewa mata sune suka fi zama abin tausayi fiye da ‘da namiji, saboda shi namiji duk yadda zaiyi ya fita domin ya nema ya sani, amma ita kuma mace sai yadda akayi da ita, idan kuma aka sami akasin haka, to wani lokaci rayuwarsu na faxawa cikin hatsari, musamman a dai dai irin wannan zamani da Allah ya kawo mu.”

“A yau inaso na sanar da ku cewa, da yardar Allah mun horar da  mata marayu har mutum 1500 akan aikin agency banking, wanda tun tuni mun kammala basu horo, kuma daga yanzu zasu fara gudanar da ayyukan su, wanda muna sa rai, a duk wata zasu sami albashi na naira dubu 70,000, wanda muna sa rai suma har zasu iya tallafa wa wasu na qasa da su.”

Da yake nasa jawabin saqon fatan alheri a wajen taron, wanda kuma shine ya wakilci gwamnan jihar kano, Dakta Abdullahi Ganduje, babban mai baiwa gwamnan jihar kano shawara ta musamman akan harkar rage fatara da raxaxin talauci wanda a turance ake kira da poverty alleviation, Malam Abdulsalaam Abubakar Sabonsara, ya bayyana jin daxinsu akan wannan shiri da kamfanin bizi ya xaukin nauyin yi wanda zai tava rayuwar al’umma, musamman marayu.

“A madadin gwamnatin jihar kano muna miqa saqon godiyarmu ta musamman ga kamfanin bizi mobile, wanda ya yi tunanin samarwa mata marayu 1500 ayyukan yi a wannan jihar, gaskiya ba muda wani abu da zamu saka maka, illa muce Allah ya biyaka, domin wannan aiki gwamnatin ka taimaka wa, domin mune haqqin al’umma ke bisa wuyanmu, amma gashi cikin ikon Allah ka fara sauke nauyin da Allah ya xaura mana.”

“Kuma a shirye gwamnatin kano take domin ta haxa hannu da kai domin ganin an inganta wannan shiri zuwa duk qananan hukumomin dake faxin jihar kano baki xaya.”

Taron dai ya sami halartar ximbin manyan al’ummar dake jihar kano, ciki har da Shugaban nin qungiyoyin marayu ta kasa reshen jihar kano, da Shugaban qungiyar fitiyanul Islam ta qara reshen jihar kano, da mai baiwa gwamnan jihar kano shawara akan harkokin sufiri, Dakta Sani Diso, da dai sauran su.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s